✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An fara zaman sulhun El-Rufai da kungiyar kwadago

Ministan Kwadago, Chris Ngige na jagorantar zaman sasanta bangarorin.

Ministan Kwadago, Dokta Chris Ngige na jagorantar zaman sasanta rikicin da ke tsakanin Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) da Gwamnatin Jihar Kaduna.

A halin yanzu, wakilan Gwamnatin Kaduna da na NLC na halartar zaman da ke gudana a Abuja.

Ngige ya shiga tsakani ne a ranar Alhamis, bayan kwana uku bangarorin biyu na kai ruwa rana ba tare da alamar sassautawa ba.

Hakan ce ta sa bangarorin suka sassauta, inda NLC ta umarci ma’aikata da su dakatar da yajin aikin ta ga abin da tattaunawar za ta haifar.

Kungiyar ta shiga yajin aiki ne bayan Gwamna Nasir El-Rufai ya sallami dubban ma’aikata bisa hujjar cewa albashin ma’aikata na cinye sama da kashi 80 na kudaden jihar.