✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An fasa kotun da ke shari’ar nadin Sarkin Zazzau

Wasu da ba a san ko su waye ba sun fasa Babbar Kotun Jihar Kaduna da ke zamanta a Dogarawa Zariya. A daren Talata ne…

Wasu da ba a san ko su waye ba sun fasa Babbar Kotun Jihar Kaduna da ke zamanta a Dogarawa Zariya.

A daren Talata ne mutanen suka fasa ofishin Babban Alkali kuton, Mai Shari’a Kabir Dabo, suka farfasa kwashe wasu takardun, kayan da yake amfani da su idan zai yi zaman kotu da sauran kayan da ba a gama tantance su ba.

A kotun ce ake saurarar karar da Iyan Zazzau Alhaji Bashir Aminu ya shigar yana kalubalantar nadin da aka yi wa sabon Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli.

Wakilin Aminiya ya tuntubi Magatakardan kotun, Jafaru domin karin bayani amma ya ce shi ba zai yi maganaba sai maigidansa ya ba shi izini.

Sai dai wasu ma’aikatan kotun sun shaida wa Aminiya cewa akwai daure kai ganin yadda aka fasa wurin cikin nasara.

Sun yi zargin yan fashin sun dauki kusan sa’a hudu dan haka Dan haka dai a yanzu an kama mai gainwurin mai suna Abubakar Tanko kuma yana ofishin ’yan Sanda ana bincike.