✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An fille kan dan shekara bakwai a Kaduna

Maharan sun kashe Fulani sannan suka fille kan wani yaro dan shekara bakwai a Kudancin Kaduna.

Maharan sun kashe wasu Fulani makiyaya uku tare da fille kan wani yaro dan shekara bakwai a Kudancin Kaduna.

Rahotanni sun ce wasu matasa ‘yan kabilar Kataf sun kai harin da ake zaton na daukar fansa ne a rugar Fulanin da ke masarautar Chawai a Karamar Hukumar Kauru mai makwabtaka da Karamar Hukumar Zangon Kataf.

Hakan na zuwa ne bayan wasu hare-hare da suka yi sanadin mutuwar mutum kusan 20 a yankin na jihar.

A zantawarsa da Aminiya, Shugaban Kungiyar Fulani Makiyaya ta Kasa reshen Jihar Kaduna, Alhaji Haruna Usman Tugga ya tabbatar da faruwar lamarin.

Alhaji Haruna ya yi kira ga Fulani makiyaya da su kwantar da hankalinsu tare da kai rahoton duk abin da ake aikata musu zuwa ga hukumomin tsaron da suka dace.

Yayin da Aminiya ta tuntubi Kakakin Rundunar ‘yan sanda na Jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige bai amsa kirar ba kuma a lokacin haxa wannan rahoto.