✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ga ’yan bindiga da rana tsaka kan babura a cikin garin Katsina

Sai dai 'yan sanda sun karyata labarin

Rahotanni daga jihar Katsina na cewa an sake ganin ’yan bindiga da rana tsaka a unguwar Sholi da ke bayan Cibiyar Lafiya ta Gwamnatin Tarayya da ke garin Katsina.

Wasu mutanen unguwar sun shaida wa Aminiya cewa sun ga wucewar ’yan bindigar a kan babura a hanyarsu ta zuwa wani wajen da ba a sani ba.

Wasu kuma na cewa ’yan bindigar sun biyo sawun wasu shanu ne a kan babura wanda ganinsu ya sa mutanen wurin suka ji tsoro, kowa ya yi ta kansa don gudun kada abin da ya faru a ranar Larabar da ta wuce ya sake faruwa da su.

Aminiya ta tuntubi jami’an asibitin da aka ce nan jama’a suka rika shiga, inda Kakakin hukumar asibitin, Alhaji Bishir yace, hakika jama’a sun shiga ciki a firgice amma babu wata alamar kawo hari a yankin balle jin karar bindiga kamar yadda wasu ke cewa an yi harbi.

Ya ce, “Kasan ance wanda majici ya sara, idan ya ga tsumma sai ya gudu. To mu dai daga abin da muka bincika, an ce an ga wasu mutane bisa babura rataye da bindiga sun bi hanyar Bypass sun wuce.

“Kawai sai wasu suka taso da wannan hayaniya wadda a yanzu haka Allah kadfai ya san wadanda suka samu rauni.”

Sai dai ita ma rundunar ’Yan Sandar jihar ta karyata labarin kai hari, kamar yadda Kakakinta, SP Gambo Isa ya shaida wa wakilin mu a lokacin da ya tuntube shi.

SP Gambo ya ce, wasu ne suka kirkiri labarin don kawo rudu a cikin jama’a.

Kakakin yayi kira ga jama’a da su guji yada labaran karya musamman masu amfani da kafofin sada zumnuta zamani da ke rubuta labaran kanzon kurege.