✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gano bom da aka dana a Gidan Yarin Oyo

Bayan kwana hudu da kai harin bom aka gano sabon bom din.

’Yan sanda sun kwance wani bom da aka gano an dana a Gidan Yarin Abolongo da ke Jihar Oyo, inda aka kai harin bom.

Mai magana da yawun Hukumar Kula da Gidajen Yari ta Kasa, Shiyyar Jihar Oyo, Olanrewaju Anjorin, ya tabbatar da rahoton.

“Gaskiya ne amma ’yan sanda sun yi nasarar kwance bom din da jami’anmu suka gano a gidan yarin,” inji shi.

An gano bom din ne kwana hudu bayan mahara sun kai harin bom a gidan yarin, suka balla shi, lamarin da ya sa daukacin fursunonin da ke tsare tserewa.

Wata majiya ta ce bom din da aka gano aka kuma kance na daga cikin wadanda maharan suka dana a harin na ranar Juma’a.