✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gano gawa 76 a hatsarin jirgin Kebbi

Rashin ingancin kayan aiki na kawo tsaiko ga aikin ceto.

Hukumomi a Jihar Kebbi sun tabbatar da gano gawarwakin fasinja 76 bayan hatsarin kwalekwalen da ya auku.

Hukumar Kula da Rafukan Cikin Gida ta Kasa (NIWA), ta sanar da hakan da kuma cewa tana ci gaba da aikin ceto, tun bayan kifewar jirgin mai dauke da fasinja kusan 200 a kauyen Tsohuwar Labata na Karamar Hukumar Ngaski ta Jihar.

“Kawo yanzu an gano gawarwaki 76; Kamar yadda muka saba muna dora laifin a kan yin lodi fiye da kima a tsoffin jiragen ruwa,” inji Jami’in NIWA mai kula da Jihar Kebbi, Birma Yusuf.

Ya ce Hukumar na da kwarewa wajen gudanar da aikin ceto, amma rashin ingancin kayan aiki na kawo musu cikas, don haka ya roki Gwamnatin Jihar Kebbi ta taimaka da kananan kwalekwale domin a samu sauki.

Zuwa daren Juma’a masu aikin ceto sun yi nasarar ceto kimanin mutum 30 da ransu daga cikin fasinjoji jirgin.

Suleman Bobo daya daga cikin masu aikin kuma Shugaban matasa garin Warra ya tabbatar wa wakilinmu.

Wakilinmu ya ziyarci wurin da ake aikin ceton bayan aukuwar hatsarin, inda ya iske daruwawan matasan garin na Warra suna kai-komo wajen gudanar da aikin ceto.

Jirgin ruwan ya kife da fasinjojin ne a yankin Tsohuwan Lambata da ke Karamar Hukumar Ngaski ta Jihar Kebbi a hanyarsa ta kai  fasinjojin Jihar Neja.