✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gano gawar ma’aikaciyar jami’a a gidanta

Makwabtan marigayiyar sun ce wari ya sa aka gano gawarta, bayan sun yi kwana hudu ba su ganta ba.

An gano gawar wata ma’aikaciyar Jami’ar Tarayya da ke Lafiya (FuLafia) mai suna Misis Angelina Tyem, wadda aka ce ta bace kwanakin baya.

Makwabta ne suka gano gawar marigayiyar a gidanta da ke Sabon Pegi a garin Lafiyan ranar Lahadi.

Wadansu makwabtan marigayiyar sun ce wari ya sa aka gano gawarta, bayan sun yi kwana hudu ba su ganta ba.

Wata majiya ta ce an caccaka mata wuka aka daddatsa ta.

Aminiya ta zanta da Shugaban Kungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’i reshen FuLafia, Mista Monday Sarki ya ce, “jin labarin ya sa muka je, sai ba mu ga mota da wayarta ba.

“Makwabta sun ce sun fara jin wari mai karfi, don haka suka fara kewayawa, inda suka hangi kofar dakin dafa abincinta a bude.

“Da muka leka sai muka hangi gawarta lamarin da ya sanya muka gayyato ’yan sanda inda suka dauki hotuna, suka yi bincike kafin a dauki gawar,” in ji shi.

Aminiya ta gano cewa marigayiyar ta tsallake rijiya da baya a wani hadarin mota mako biyu da suka wuce a hanyar Akwanga zuwa Jos.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Nasarawa, ASP Ramhan Nansel ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce za su gudanar da bincike a kai.