✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gano gawar mutum 16 a hatsarin jirgi a Kebbi

Ana ci gaba da aikin ceto mutanen da suka bace.

Hukumomi sun gano gawar mutum 16, wasu mutum shida Kuma suka bace sakamakon hatsarin jirgin ruwan a Karamar Hukumar Koko/Besse a Jihar Kebbi.

Gwamnan jihar, Atiku Bagudu da Ministan Shari’a, Abubakar Malami sun kai ziyarar jaje yankin don nuna alhininsu game da faruwar lamarin.

Bagudu ya yi addu’ar Allah Ya jikan wadanda suka mutu tare da bai wa iyalansu hakurin rashinsu.

Gwamnan ya kuma yaba wa wadanda suka sadaukar da lokacinsu don aikin ceto mutanen da lamarin ya rutsa da su.

Sannan ya gargadi masu jiragen ruwa da guje wa tafiyat dare da kuma yin lodi da ya wuce kima tare da kuma daukar matakan kariya.

Shugaban karamar hukumar, Alhaji Yahaya Bello, ya gode wa gwamnan kan karamcin da ya yi wa al’ummar yankin na kai musu ziyarar jajen.

Aminiya ta ruwaito cewar jirgin ya yi hatsarin ne a ranar Talata, a lokacin da yake dauke da manoman shinkafa kimanin 100 zuwa kauyen Samanaji.

Tuni aka ceto mutum 80 yayin da hukumomin agaji da masu aikin ceto ke ci gaba da kokarin gano mutum shida da suka bace.