✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gano gawar mutum 30 da aka yi garkuwa da su a wani asibiti

An gano gawarwarkin a wani tsohon asibitin gwamnati da masu garkuwa da mutane suka mayar maboyarsu

An gano gawar wasu mutum 30 da aka yi garkuwa da ’yan bindiga suke jefar a wani tsohon asibiti da aka daina amfani da shi a Jihar Ribas.

An gano gawarwakin ne bayan sun rube a kangon asibitin da aka daina amfani da shi a yankin Elele Alimini a Karamar Hukumar Emohua ta jihar.

Shugaban Karamar Hukumar Emohua, Chidi Lyold, shi ne ya sanar da gano rubabbun gawarwakin mutanen da aka yi garkuwa da su, a lokacin da ya jagoranci jami’an tsaro domin farautar masu haramtattun kananan matatun mai a yankin.

Bayan ganin rubabbun gawarwakin ne, “Shugaban Karamar Hukumar ya sa aka bincike tsohon asibitin, inda aka gano gungun masu garkuwa da mutane da kuma masu masu amfani da wurin a matsayin maboyarsu,” a cewar Kakakin Shugaban Karamar Hukumar, Bright Elendu.

Ya ce shugaban karamar hukumar ya bayyana matukar kaduwa da ganin rububbun gawarwakin da ake kyautata zaton na mutanen da aka yi garkuwa da su ne.

Wasu majiyoyi sun ce masu garkuwa da mutane ne suke a amfani da kangon tsohon asibitin a matsayin maboyarsu.

Elendu ya ce shugaban karamar hukumar ya kuma sa an tsare wasu masu haramtattun kananan matatun mai a yankin a lokacin samamen.