✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

An gano hakorin dan Adam da ya shekara miliyan 1.8

Jojiya wuri ne mai muhimmanci ga ilmin burbushin halittu.

Wasu masana Ilimin Kimiyyar Kayan Tarihi sun gano wani hakorin dan Adam a Jojiya da ke kasar Amurka, da ya kai shekaru miliyan 1.8.

Wannan binciken nasu ya tabbatar na mutane farko-farko ne da suka yi rayuwa a nahiyar Turai.

An gano hakorin a kusa da kauyen Orozmani mai tazarar kilomita 100 daga Kudu maso Yammacin Tbilisi, babban birnin Jojiya da kuma kusa da Dmanisi.

A garin na Dmanisi ne a karshen shekarar 1990 zuwa farkon 2000, aka gano kokon kawunan mutane wadanda aka yi hasashen sun kai shekaru miliyon 1.8. a karkashin kasa.

Binciken ya gano cewa, mutanen sun yi rayuwa a shekarun da suka shude bayan sun yi kaura daga nahiyar Afrika.

Wani bincike na baya-bayan nan da aka gudanar ya nuna cewa, yankin Kudancin Caucasus mai tuddai da yawa, ya kasance daya daga cikin wuraren da mutanen farko suka fara zama bayan sun bar Afirka.

Shugaban masu binciken Giorgi Bidzinashbili ya ce, suna hasashen hakorin na daya daga kabilar Zezva ko Mzia ne, wadanda a baya aka gano kokon kawunansu, wanda ya nuna sun yi rayuwa a baya sama da shekaru miliyon 1.8 a yankin.

Da yake magana da manema labarai game da binciken, dalibin ilmin kimiyyar kayan tarihi, Jack Peart, wanda ya gano hakorin ya ce, “Abubuwan da ke faruwa ba a wannan waje ba ne kadai, inda mutanen da suka bar Afirka shekaru miliyan 1.8 da suka shude.

“Yana tabbatar da cewa Jojiya wuri ne mai muhimmanci ga ilmin burbushin halittu da kuma labarin dan adam gaba daya.