✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gano karamar jakar mace bayan shekara 54 da bacewa

An gano jakar ne bayan ta bace da shekara 54 a Virginia.

Wata mata da ke zaune a West virginia ta kasar Amurka ta sake samun jakarta da ta rasa a lokacin da take rawa a makaranta kusan shekara 55 da suka gabata.

Matar mai suna Sharon Day ta ce tana da shekara 16 a duniya lokacin da ta rasa karamar jakar a bikin rawa na makarantar Fayetteville High School a 1968, kuma ba ta sa ran za ta sake ganin jakar ko kayan da suke cikinta ba.

An rufe makaranta kwata-kwata a shekarar 2019, kuma ma’aikatan da suke aiki da Kamfanin New River Contracting sun ce sun ji mamaki lokacin da jakar hannun ta fado daga wani bututun na’urar sanyaya daki a lokacin da suke gyara ginin da aka mayar da shi gidajen zama.

Mai kamfanin gine-ginen, Mista Bradley Scott, ya ce bututun ya farfashe shekara da shekaru kuma a cikinsa an gano wasu kayayyaki da dama da suka bace.

“Akwai tsofaffin takardun dauka a makaranta da tikitin kallon damben boksin da sauran wasu kayayyaki da suka rika fadowa lokacin da muka fasa shi muka bude shi a karon farko a shekara 100,” Scott ya shaida wa kafar talabijin ta WvvA-TV.

Scott ya yi amfani da kafafen sadarwar zamani don ganin ko zai iya gano mai jakar.

“Ganin hotunan da suke cikin jakar da sunan da ke bayan hotunan da takardun inshora da suke ciki, sai na rika ji a raina cewa tabbas za mu iya gano mai jakar,” in ji shi.

Bayan mako guda Scott ya gano matar ta hanyar bincike a shafin Facebook.

“Abu ne da ban taba tunanin zan gani ba,” in ji Misis Day.

Ta ce, tana shirin ta juya hotunan da sauran kayayyakin da suke cikin jakar zuwa wani littafin karatu na yara don adana tarihi.