✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An gano karin gawargwaki 21 a hatsarin jirgin ruwan Girka

Kusan mutum 37 ne ake fargabar sun bace a hatsarin

Jami’an tsaron gabar tekun Girka sun ce sun gano gawarwaki 21 daga cikin kwale-kwalen bakin-haure biyu da suka nitse a farkon makon wannan makon.

A ranar Laraba jami’an suka ce an gano gawarwaki 20 a kusa da tsibirin Evia, kwana guda bayan wani jirgin ruwa da ake kyautata zaton yana dauke da mutane kusan 70 ya nutse a cikin tekun da ke cike da hadari.

Kamfanin Dillancin Labaran Faransa (AFP) ya rawaito cewa, an kuma gano wata gawar a ranar Talata a wani hatsarin da ya auku a tsibirin Samos na kasar, inda wani jirgin ruwa daga gabar tekun Turkiyya ya kife dauke da mutane 12.

Sama da mutane 30 ne ake fargabar sun bace a hatsarin Evia, yayin da wasu bakwai suka bace a Samos.

Tun farko, jami’an tsaron gabar tekun sun tabbatar da mutuwar mutane 14 bayan aukuwar hatsarin.

Galibi, kasashen Girka da Italiya da Spaniya ne wuraren da bakin-haure musamman daga Afirka da Gabas ta Tsakiya ke zuwa don neman  ingantacciyar rayuwa.