An gano maboyar ‘yan bindiga a Zamfara | Aminiya

An gano maboyar ‘yan bindiga a Zamfara

    Abubakar Muhammad Usman

Rahotanni sun tabbatar da cewa an gano wata maboyar ‘yan bindiga da suka addabi yankunan Karamar Hukumar Tsafe a Jihar Zamfara.

Shugaban karamar hukumar, Alhaji Aminu Mudi Tsafe ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai  a ranar Litinin.

A cewarsa, “Lokacin da ‘yan bindiga suka kai hari a ranar Lahadi, dakarun soji sun bi bayansu, inda a nan ne suka gano maboyar tasu”.

“Sanin maboyar ta su zai taimaka mana wajen farmarkarsu tare da lalata maboyar tasu, kuma tuni jami’an tsaro sun fara shirin tunkararsu” a cewarsa.

A ranar Lahadi ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari Karamar Hukumar Tsafe  inda suka kashe mutane da dama, ciki har da dan gidan tsohon Mataimakin Sifeto Janar na ’yan sanda, Mamman Tsafe.