✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gano matattun kyanwoyi 100 a gidan wani tsoho

Akwai kuma kuregu da beraye, da muka-mukin karnuka da dama da aka samu.

Kungiyoyin kare dabbobi a kasar Faransa sun ce, sun gano matattun kyanwoyi 100 a gidan wani tsoho mai shekara 81 a Kudancin Faransa.

’Yar uwar mutumin ce ta sanar da ’yan agajin inda suka shiga gidansa, bayan da aka kai shi asibiti a birnin Nice da ke yankin Ribiera na Faransa sannan aka gano gawar kyanwoyin.

Yawancin kyanwoyin sun mutu ne aka adana gawarwakinsu ta hanyar nade jikinsu da aka sa a cikin akwatunan katako kamar yadda jaridar Nice-Matin ta yankin ta ruwaito.

Baya ga kyanwoyin da aka samu a ciki da wajen gidan, akwai kuma kuregu da beraye, da muka-mukin karnuka da dama.

Kuma an iske kyanwoyi 20 a cikin yunwa da aka ceto su daga gidan aka mika su ga likitocin dabbobi don samar yi musu jinya da kai su gidajen kula da dabbobi.

Shugaban Kungiyar La Tribu du Fourmilier, Mista Philippe Desjackues, ya shaida wa kafar Labarai ta AFP cewa, “Idan aka yi la’akari da matsayinsu, yawancin kyanwoyin sun mutu ne kafin a sa su a cikin akwatunan.

“Amma muna tsammanin akalla biyu an kulle su da ransu.”

An tsinci gawar kyanwa daya a kan gadon dakin saukar baki na mamallakin dabbobin, a wani bangare kuma akwai alamun an cinye wasu kyanwoyin.

Mista Desjackues ya ce, mai yiwuwa tsohon wanda dan fansho ne yana da dabi’ar tara dabbobi masu yawa a gidan.

Galibin masu yin haka sukan yi ne saboda kadaici, ba tare da suna iya kula da bukatun dabbobin ba.

Mista Desjackues ya ce, kungiyoyin kare dabbobin za su shigar da tuhumetuhume a kan mutumin saboda rashin kula da dabbobin da kuma sakaci, idan ya samu lafiya.