✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An garkame rassan bankin GT 5 a Kano saboda kin biyan haraji

Hakan ya biyo bayan kin biyan harajin da ya kai sama da Naira biliyan daya da bankin ya yi.

Hukumar Tattara Haraji ta Jihar Kano (KIRS) a ranar Talata ta garkame wasu rassan bankin GT saboda kin biyan haraji na tsawon shekaru shida.

Rufewar ta biyo bayan wani umarnin Babbar Kotun Jihar Kano kan matakin bankin na kin biyan haraji tsakanin shekarun 2014 zuwa 2019, wanda ya kai sama da Naira biliyan daya.

Rassan bankunan da matakin ya shafa dai sun hada da Shalkwatar Shiyya ta bankin dake kan titin Murtala Muhammad da reshen Wapa, da na titin France Road, da na kan titin zuwa Zariya da kuma na anguwar Bachirawa.

Daya daga cikin rassan bankunan na GT da aka rufe

Da yake jawabi ga ’yan jarida yayin zagayen rufe bankunan, Daraktan Shari’a na hukumar, Barista Bashir Yusuf Madobi ya ce kunnen uwar shegun da bankin ya yi ne na ba hukumarsu wasu takardun bayanai ya tilasta musu daukar matakin.

Ya ce, “Kin ba mu wadannan takardun da za mu tantance nawa ya kamata su biya ne ya bata mana rai

“Mun maka su a gaban Babbar Kotun Kano saboda mu sami damar karbo dukkan hakkokin da suka kamata.

“Dalilin kenan da ya sa yau muka je muka rufe wadannan rassan bankin, wanda hakan ya yi daidai da tanade-tanaden dokokin karbar haraji na kasa,” inji Barista Bashir.

Reshen bankin GT dake Wapa wanda shima aka rufe
Reshen bankin GT dake Wapa wanda shima aka rufe

A kan sharadin sake bude bankunan kuwa, KIRS ta ce dole bankin na GT ya biya akalla kaso 25 cikin 100 na harajin sannan kuma ya ba hukumar takardun data bukata.

Kazalika, dole bankin ya biya kaso 10 cikin 100 na harajin a matsayin hukuncib da aka tanadarwa duk wanda ya ki biyan haraji har sai da aka je gaban kotu.

To sai dai yunkurin Aminiya na jin ta bakin bankin ya ci tura saboda dukkan Manajojin rassan da lamarin ya shafa sun ce ba su da hurumin tsokaci a madadin bankin.

Rufe bankunan dai ya tilastawa abokan huldarsu da suka yi sammako komawa gida bayan rufewar.