✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An garzaya asibiti da mahaifin gwamnan Nasarawa

An killace mahaifin Gwamnan Jihar Nasarawa Alhaji Sule Bawa bayan an garzaya da shi asibiti. Alhaji Sule Bawa shi ne kuma Sarkin yankin Gudi da…

An killace mahaifin Gwamnan Jihar Nasarawa Alhaji Sule Bawa bayan an garzaya da shi asibiti.

Alhaji Sule Bawa shi ne kuma Sarkin yankin Gudi da ke Karamar Hukumar Akwanga a jihar Nasarawa.

Wani mazaunin yankin Gudi da ya nemi a boye sunansa ya ce, “Sarkin Gudi Alhaji Sule Bawa na fama da zazzabi ne kafin daga bisaniya fara tari.

“Hakan ta sa aka garzaya da shi Asibitin Kwararru na Dalhatu Araf (DASH) da ke garin Lafia a ranar Laraba.

“Ranar Alhamsi tawagar jami’an lafiya sun yi feshin kashe kwayoyin cuta a gida da fadar mahaifin gwamnan,” inji shi.

Majiyarmu ta ce babu tabbacin ko cutar coronavirus ce ta kama basaraken, wanda jama’a ke yawan kai wa ziyarar girmamawa, musamman a ranar kasuwa.

Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin Asibitin, sai dai sun bayyana cewa ka’idar aikinsu ba ta yarda a bayyana sunan mara lafiya ba.

Gwamna Abdullahi Sule ya sha nanata cewa, a Abuja ake yin gwajin cutar coronavirus ga wadanda aka dauki jinsu daga jihar Nasarawa.