✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu hukunta likitocin da ke yajin aiki —Minista

Tattaunawar likitoci da Gwamnatin Tarayya ta gaza cimma matsaya a kokarin gwamnatin na kawo karshen yajin likitocin da suka fara. A ranar Litinin 15 ga…

Tattaunawar likitoci da Gwamnatin Tarayya ta gaza cimma matsaya a kokarin gwamnatin na kawo karshen yajin likitocin da suka fara.

A ranar Litinin 15 ga watan Yuni ne Kungiyar Likitoci Masu Neman Kwarewa ta Kasa (NARD) ta tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani.

NARD ta dakatar da dukkan ayyukan kula da marasa lafiya, ciki har da na gaggawa da kuma kula da masu cutar coronavirus.

Kungiyar wadda gammaya ce ta kungiyoyin likitoci, ta ce ta dauki matakin ne saboda halin rashin kulawa da rashin kayan aiki da likitoci ke fama da su musamman masu kasadar kula da masu cutar coronavirus.

Bayan shafe sa’o’i shida bangarorin na tattaunawa a ranar Talata, wakilan NARD suka fice daga taron ba tare da cimma matsaya ba.

A shirye muke, gwamnati muke jira – Likitoci

Shugaban NARD Aliyu Sokomba ya shaida wa wakilinmu cewa suna jiran gwamnati ne ta yi abin da ya dace domin su a shirye suke su janye yajin aikin.

“Za mu janye yajin aikin da zarar gwamnati ta yi wani abu kwakkawara. Tana yin hakan mu kuma za mu janye yajin aiki cikin sa’a 24, inji shi.

Za mu dauki mataki – Minista

A nasa bangaren Ministan Lafiya, Osagie Ehanire, wanda ya nuna bacin rai game da matakin likitocin ya ce gwamnati ta dauki lafiyar ‘yan Najeriya.

“A shirye muke mu kare rayukan ‘yan Najeriya don haka ba za mu yarda asibitoci su zauna babu likitoci ba”, inji shi.

Ya ce don haka daga 7.00 na safe ranar Laraba za a bude rijistar rubuta sunayen likitocin da ke zuwa aiki a asibitoci kuma duk wadanda ke fashi za su dandana kudarsu.

Ehanire ya koka cewa Najeriya ce kasa ta farko a duniya da likitoci ke tafiya yajin aikin yayin da ake fama da annobar da ta addabi duniya.

Dalilin yajin aikin

Kungiyar NARD wadda gammaya ce ta kungiyoyi likitoci a Najeriya na yajin akin ne saboda rashin isasshen albashi da kuma kayan kariya musamman ga likitocin da ke yaki da cutar coronavirus.

Shugaban NARD, Aliyu Sokomba ya ce gwamnati ta gaza cika sharudan da aka gindaya mata, musamman na kara albashin likitocin da ke cikin barazanar kamuwa da cutar.

Likitoci sun yi gargadi a baya

A kwanakin baya dai kungiyar likitocin ta ce yajin aikin ya zama wajibi saboda mawuyacin halin da mambobinta suke ciki.

Shugaban kungiyar wadda ke matsayin uwar kungiyoyin likitocin asibitocin gwamnati ya kuma ce “Yajin aikin namu na sai baba-ta-gani ne.

“Babu wanda zai fito aiki, kama daga masu jinyar masu cutar COVID-19 zuwa masu kula da wasu cututtuka da ke bukatar kulawar gaggawa.

“Mun umarci dukkan likitoci da sauran manyan ma’aikatan lafiya cewa su ma su bi sahu da zarar an fara yajin aikin”, in ji sanarwar.

Kungiyar ta kuma jajanta wa ‘yan Najeriya kan irin halin da za su iya fadawa da zarar ta fara yajin aikin a mako mai zuwa.

Ta kara da yin Allah-wadai da irin halin ko-in-kula da ta ce gwamnati ke nuna wa bangaren lafiya na kasar.

Ta kuma koka kan mawuyacin yanayin aiki da mambobinta ke ciki musamman wadanda ke aiki a cibiyoyin lafiya mallakar jihohi.

Ko a kwanakin baya sai da reshen Babban Birnin Tarayya na kungiyar ya shiga yajin aikin a farkon bullar annobar a Najeriya bisa dalilan kin biyan hakkoki ma’aikatan lafiya.