✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An girke jami’an tsaro 10,000 domin zaben kananan hukumomin Kano

Babu zirga-zirga daga karfe 6 na safe zuwa 6 na yamma a ranar zaben.

Jami’anta tsaro 10,000 ne aka girke domin tabbatar da doka da oda a zaben Kananan Hukumomin Jihar Kano da za a gudanar ranar Asabar 16 ga Janairu, 2021.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna, ya ce jami’an sun kunshi ’yan sanda 7,251 da sauran jami’an taro sama da 2,000.

“A shirye muke mu tabbatar da ganin zaben ya gudana cikin lumana kuma ba za ta lamunci duk wani yunkuri na tayar da zaune tsaye ba.

“Duk wanda aka kama yana neman tayar da fitina zai yaba wa aya zaki,’’ inji sjhi.

DSP Abullahi Haruna ya ce za a tura jami’an tsaron ne zuwa gundumomi 484 da ke fadin kananan hukumomin Jihar Kano 44.

Ya ce sauran hukumomin tsaron sun hada da jami’an Hukumar Tsaro ta NSCDC, Hukumar Shige da Fice, Hukumar Kwastam da Hukumar Kula da Gidjen Yari da sauransu.

Ya kara da cewa za a dakatar da zirga-zirga daga karfe shida na safe zuwa shida na yammacin ranar Asabar, amma ba zai shafi masu muhimman ayyuka ba.

Rundunar ta byaba wa jama’ar Jihar bisa hadin kan da suke ba ta, wadda ya ce a shirye take ta tabbatar da tsaro da oda, kafin, a lokacin, da kuma bayan zaben.