✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

An gurfanar da magidanci a kotu kan caka wa surukinsa kwalba

Ta ce wanda ake zargin ya daba wa mahaifin matarsa wata fasasshiyar kwalba a kai

An gurfanar da wani magidanci a gaban wata Kotun Majistare mai zamanta a Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun, kan zargin daba wa surukinsa kwalba a kai.

Lauyan mai gabatar da kara, Sufeta Evelyn Motim, ta fada wa kotun cewa, mai kare kansa ya aikata laifin ne ranar 30 ga watan Oktoba a yankin Abule Ijaye da ke jihar.

Ta ce wanda ake zargin ya daba wa mahaifin matarsa wata fasasshiyar kwalba a kai.

Ta ce surukin ya gamu da iftila’in ne bayan da aka gayyato shi don ya zo ya sasanta matsalar aure, daga nan wanda ake zargi ya hada baki da wasu suka lakada wa surukin duka.

Lauyar ta ce wannan laifi ne da ya saba wa sassa na 516 da 355 na Kundin Dokokin Manyan Laifuka na Jihar Ogun na 2006.

Alkalin kotun ya ba da umarnin a kai wanda ake zargin kurkuku a ajiye zuwa lokacin da zai biya kudin beli N50,000 da aka yanka masa da kuma shaida daya.

Daga nan, ya dage shari’ar zuwa 23 ga Nuwamba don yanke hukunci.

(NAN)