Daily Trust Aminiya - An gurfanar da mahaifin da ya yi lalata da ‘ya‘yansa mata uk
Subscribe

An gurfanar da mahaifin da ya yi lalata da ‘ya‘yansa mata uku

Wata Kotun Majistire da ke Fatakwal, ta ba da umarnin tsare Uchenna Tobias, mahaifin da aka kama da zargin lalata da dukkanin ‘ya‘yansa mata uku masu kananan shekaru.

An gurfanar da Tobias a gaban Kotun, bayan mai dakinsa mai shekaru 38 ta kai wa ‘yan sanda kararsa tana mai cewa “ya saba lalata da ‘ya‘yansu mata; ‘yar wata tara, ‘yar shekara biyar da ‘yar shekara 10 tun babbar cikinsu tana da shekaru biyu kacal a duniya.”

Yayin zaman Kotun da aka gudanar a ranar Alhamis, Mai Shari’a Amaka Amanze ta umarci Rundunar ‘yan sanda su sauya wa laifin da ake tuhumar Tobias daga na cin zarafi zuwa na lalata.

Haka zalika Jami’ar Ignatius Ajuru da ke Fatakwal, ta dakatar da wani Malami, Dokta Rowland Igwe, da ya ci zarafin wata daliba har ta kai a samun juna biyu.

A rahoton da jaridar Vanguard ta wallafa, Shugaban Jami’ar, Farfesa Ozo-mekuri Ndimele, ya sanar da hakan cikin wani sako da ya wallafa kan shafinsa na Facebook.

More Stories