✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gurfanar da matashi kan tayar da zaune tsaye 

An gurfanar da wani matashi mai shekara 29 a gaban Kotun Majistare da ke Ado-Ekiti kan tayar da husuma.  Matashin, ana tuhumar sa ne da…

An gurfanar da wani matashi mai shekara 29 a gaban Kotun Majistare da ke Ado-Ekiti kan tayar da husuma. 

Matashin, ana tuhumar sa ne da laifukan takura wa jama’a da tayar da husuma da barazanar kunna wutar rikici.

Dan sanda mai gabatar da kara, Insp. Johnson Okunade, ya shaida wa kotun cewa matashin ya aikata laifin ne a ranar 18 ga watan Fabrairun 2021 a layin Bamgboye da ke Ado-Ekiti.

Okunade, ya ce wanda ake tuhumar ya yi nemi tayar da husuma ta hanyar yi wa wanda ya kawo karar sa barazanar ji masa rauni saboda wani dalili da ba a bayyana ba.

Jami’in dan sandan ya ce hakan ya saba da Sashe na 249 da 86(1) na kundin dokokin hukunta manyan laifuka na Jihar Ekiti na shekarar 2012.

Ya kuma bukaci kotun da ta dage zamanta don ya samu damar gabatar mata shaidu.

Sai dai matashin ya musanta zargin da ake tuhumar sa a kai.

Lauyan wanda ake kara, Busuyi Ayorinde, ya bukaci kotun da ta ba da belin sa tare da alkawarin ba zai karya sharudan belin ba.

Alkalin kotun, Mai shari’a Adedayo Oyebanji, ya ba da belin matashin kan kudi N100,000 tare da kawo mutum guda da zai tsaya masa.

Oyebanji ya ce wajibi ne wanda zai tsaya masa ya kasance ya mallaki fili a yankin da kotun ke da hurumi.

Alkalin ya kuma dage zaman kotun zuwa ranar 7 ga watan Afirilu mai zuwa.