✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gurfanar da matashi kan zargin satar akuya

Akuyar da aka samu a tare da matashin ta sata ce.

Wata Kotun Majistire da ke zamanta a birnin Ado-Ekiti na Jihar Ekiti, ta gurfanar da wani matashi da aka kama da wata akuya da ake zargi ta sata ce.

Matashin mai shekaru 29 wanda aka gurfanar a ranar Laraba, jami’an yan sanda na zarginsa da dan hali kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito.

Sufeta Oriyomi Akinwale, jami’in dan sanda mai shigar da kara a gaban kotu,  ya ce matashin mai suna Abubakar Muhammad ya aikata laifin da ake tuhumarsa da shi da misalin karfe 10.00 na safiyar ranar 18 ga watan Maris a Ado-Ekiti.

Ya yi zargin cewa akuyar da aka samu a tare da matashin ta sata ce, yana mai cewa irin wannan laifi yana cikin karo da sashe na 430 cikin Kundin Dokokin Miyagun Laifuka na Jihar Ekiti da aka yi wa kwaskwarima a 2012.

Sufeta Akinwale ya bukaci kotun ta dage zaman sauraron karar domin samun wadataccen lokacin zurfafa bincike a kan lamarin da kuma hujjoji.

Sai dai matashin bai amsa laifin da ake tuhumarsa da shi ba, inda lauyansa, Mista Tunmise Akinwumi ya nemi kotun ta karbi bukatun bayar da belin wanda yake karewa a bisa tanadin da doka ta yi.

Da wannan ne alkalin kotun mai shari’a Bankole Oluwasanmi ya amsa kiran lauyan wanda ake tuhuma, inda ya bukaci a biya Naira 25,000 a matsayin beli tare da gabatar da mutum daya wanda zai tsaya masa.

Mai shari’a Oluwasanmi ya dage sauraron karar zuwa ranar 5 ga watan Mayun 2022.(NAN)