✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An gurfanar da su a kotu kan wulakanta gawa

Sai dai babu wani cikakken bayani kan yadda aka yi aka kai gawar shagon, da kuma ko sun aikata mata wani rashin da’a.

An gurfanar da wasu mutum biyu a gaban wata Kotun Majistare mai zamanta a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo, kan zargin wulakanta wata gawa.

Kamfanin Dillancincin Labarai na Najeriya (NAN), ya rawaito ana tuhumar mutum biyun ne da aka gurfanar ranar Juma’a da hadin baki wajen wulakanta gawar ta hanyar jefar da ita a wani shago.

Sai dai babu wani cikakken bayani kan yadda aka yi aka kai gawar shagon, da kuma ko sun aikata mata wani rashin da’a.

Lauyar mai tuhuma, ASP Foluke Adedosu, ta shaida wa kotun cewa, an aiktata laifin ne ran 12 ga Satumba, laifin da ta ce ya saba wa sassa na 516 da 242(1)(b) na Kundin Dokokin Manyan Laifuka na Jihar Oyo, na 2000.

Sai dai masu kare kansu sun musanta zargin da ake yi musu.

Tuni dai Alkalin kotun, Mai Shari’a O. A Enilolobo, ta ba da belin wadanda ake tuhumar kan N100,000 ga kowannensu da kuma shaida dai-daya.

Kotu ta dage shari’ar zuwa ranar 21 ga Fabrairu mai zuwa.

(NAN)