✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gurfanar da mutum 5 a gaban kotu kan cin naman mutum a Zamfara

Ana dai zarginsu ne da kashewa da cin naman wani yaro mai kimanin shekara tara a duniya.

A Jihar Zamfara, an gurfanar da wasu mutum biyar a gaban kotun majistare mai lamba daya a Gusau ranar Talata, bisa zarginsu da kashewa tare da cin naman wani yaro.

Daga cikin wadanda aka gurfanar ɗin kuma ake zargi, har da wani fitaccen dilan motoci a Jihar.

Ana dai zarginsu ne da kashewa sannan suka ci naman Ahmad Yakubu Aliyu, wani yaro mai kimanin shekara tara a duniya.

Daya daga cikin mutanen da aka gurfanar a gaban kotun.
Daya daga cikin mutanen da aka gurfanar a gaban kotun.

An dai kawo mutanen da ake zargi ne gaban kotun cikin tsauraran matakan tsaro.

Sai dai bayan da alkalin kotun, Mai Shari’a Sa’adu Gurbin Bore ya karanta musu laifukan da ake tuhumarsu da su, sun musanta aikatawa.

Daga nan ne ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar takwas ga watan Fabrairun 2022 mai zuwa.

Iyayen yaron da sauran masu jajanta musu dai sun yi cincirindo a harabar kotun suna neman a hukunta wadanda ake zargin, inda suka ce lamarin abin takaici ne matuka.

Mahaifiyar yaron, wacce ta bayyana sunanta a matsayin Jamila Abdurrahman, ta shaida wa Aminiya cewa sun je kotun ne don bin kadin jinin dan nasu, da kuma tabbatar da cewa bai tafi a banza ba.

Daga nan ne sai alkalin kotun ya aike da mutum uku daga cikin wadanda ake zargin zuwa gidan gyaran hali, yayin da ragowar biyun kuma ya aike da su gidan horar da kangararrun yara saboda karancin shekarunsu.