✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gurfanar da shi a gaban kotu kan zargin zambar kudi N1.8m

’Yan Sanda sun gurfanar da wani mutum a gaban Kotu kan zargin zambar kudi har N1.8m

Jami’an ’Yan Sanda a jihar Ekiti sun gurfanar da wani mutum mai kimanin shekaru 46 a duniya a gaban Kotun Majistare dake birnin Ado-Ekiti kan zargin zambar kudi har N1.8m

Mutumin, wanda ba a bayyana adireshinsa ba, ana tuhumarsa ne da aikata zamba cikin aminci, duk da cewa ya musanta tuhumar da ake yi masa a gaban kotun.

Dan sanda mai gabatar da kara a gaban kotun, Oriyomi Akinwale, ya shaidawa kotun cewa mutumin da ake zarga ya aikata laifin ne a watan Febarairun 2018 da misalin karfe 09:00 a wurin Makarantar Mishan dake yankin unguwar Fabian a birnin Ado-Ekiti.

Oriyomi, yace an kama shi yana dauke da zunzurutun kudi har Naira miliyan daya da dubu dari takwas mallakar wani mutum mai suna Mista Salami Tajudeen kan cewa zai siyar masa da wani kango.

Dan sandan ya ce, aikata irin wannan laifin ya saba da tanade-tanaden sashe na 419 na Kundin Dokokin Manyan Laifuka na jihar Ekiti na shekarar 2012.

Ya kuma bukaci kotun da ta dage sauraran karar don ya kara samun damar nazartar lamarin dama samar da shedu.

Sai dai lauyan da ke kare wanda ake zargi, Mista Idowu Owoeye, ya bukaci kotun da ta bayar da belin wanda ake tuhuma tare da bayar da tabbacin ba zai karya ka’idojin da za a shimfida bayan bayar da belin ba.

Da yake yanke hukunci, alkaliyar kotun, Mai Shari’a Dolapo Fasuba, ta bayar da belin mutumin kan kudi N50,000 da kawo wani mutum daya da zai tsaya masa.

A karshe Alkalin ya dage zaman kotun har zuwa ranar 16 ga watan Maris din 2021 don ci gaba da sauraron karar.