✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan matan da ke yunkurin ‘kashe gwamna’ sun gurfana a kotu

Ana zargin ’yan mata da harbin bindiga da neman kashe Gwamnan Osun, Gboyega Oyetola.

An gurfanar da wasu ’yan mata biyu gaban kotun bisa zargin yunkurin kashe Gwamnan Adegboyega Oyetola na Jihar Osun.

Dan sandan mai gabatar da kara John Idoko ya shaida wa Kotun Majistare mai zamanta a Osogbo cewa ’yan matan na daga cikin mutanen da suka fasa babban shagon kasuwanci a garin.

Ya ce an hada baki da su aka yi yunkurin kashe gwamnan ta hanyar harbi da bindiga da kuma jifa da duwatsu.

Dan sandan ya ce ’yan matan sun fasa wani babban shagon na Ashiru Ibrahim Olayrmi, suka sace kwamfuta da wayoyin hannu da darajarsu ta kai N3,568,000.00.

Laifukan a cewarsa, sun saba da kundin laifuka na jihar na 2020 karkashin sashi na 516, 320 (1) da 451, 414 da kuma 390.

Wadanda ake zargin sun musanta aikata abin da ake tuhumar su da aikatawa sannan lauyansu ya bukaci kotun da ta ba da su beli.

Amma alkalin kotun, Mai Shari’a Olusegun Ayilara, ya hana tare da umartar a ci gaba da tsare su a kurkuku na Ilesa zuwa ranar 20 ga watan Nuwamba 2020.