✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gwangwaje zawarawa da tallafin shinkafa da tsabar kudi

Wasu mata zaurauwa sun amfana da tallafin buhunan shinkafa da tsabar kudi don rage musu radadin talaucin da suke ciki sakamakon kullen COVID-19 a garin…

Wasu mata zaurauwa sun amfana da tallafin buhunan shinkafa da tsabar kudi don rage musu radadin talaucin da suke ciki sakamakon kullen COVID-19 a garin Iresi na Jihar Osun.

Zawarawan da suka samu kayan da Adekemi Adejare ta raba, sun bayyana cewa tallafin da gwamnatin jihar ta raba na kayan abinci a lokacin kullen COVID-19 bai kai gare su ba.

Shugabar wata kungiyar mata Musulmi a yankin, Alhaja Balkis Agboola tare da Deceaness Rebecca Oguntomi wanda ta yi bayanin a madadin mata Kiristocin yankin sun yi godiya ga Adejare bisa rabon tallafin.

Sun ce za su yi amfani da shinkafar da kudin da aka ba su wurin yin shagalin bikin Kirsimeti da na shiga sabuwar shekara tare da addu’ar Allah Ya saka wa wadda ta ba su tallafin da alheri.

Adekemi Adejare, wadda ita ce ta assasa shirin muhawara a fannin ilimi a nahiyar Afirka na ADEP, ta ce zabi ta raba kayan a Iresi ne saboda a nan ta taso kuma tana da burin tallafa wa zaurawan yankin saboda halin da suke ciki.

“A nan na taso kuma ina kaunar mutanen yankin. Zan yi amfani da kungiyata da ba ta gwamnati ba, da ke shirya muhawara a fannin ilimi a Afirka (ADEP), in tallafa wa zawarawan yankin saboda sun taimake ni a lokacin da nake tasowa.

“Ina sane da cewa babban nauyin da ke kan zaurawan shi ne yadda za su ciyar da iyalansu.

“Shi ya sa na siyo abincin na rasa musu, sanya musu farin ciki shi ne babban burina kamar yadda kuke gani; wadannan zawarawan mabukata ne kuma ba su da mai taimaka musu.

“Tallafin ba shi da yawa, kawai na yanke shawarar bayarwa ne a raina kuma ina da masaniyar cewa za su jima suna farin ciki da wannan.

“Ina fatan za mu ninka wannan a nan gaba kuma ina da burin shirya duba marasa lafiya da ba su magani har sai an tabbatar sun samu lafiya”, kyauta.