✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An haifa wa Osinbajo jika na farko

Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya shiga sahun kakanni bayan da diyarsa Oludamilola ta haifi da namiji. Oludamilola ta haifi jikan farko a duniya…

Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya shiga sahun kakanni bayan da diyarsa Oludamilola ta haifi da namiji.

Oludamilola ta haifi jikan farko a duniya ga Mataimakin Shugaban Kasar ne ranar Litinin.

Mataimakin Shugaban Kasar da kansa ya wallafa bayanin hakan a shafinsa na Twitter da misalin karfe 4.16 na yammacin Litinin.

“Daukaka ta tabbata ga Ubangiji! A yanzu na zama kaka!

“Diyata, Oludamilola da mijinta Oluseun sun zama iyaye kasancewar sun samu karuwar da namiji da safiyar yau,” inji Osinbajo.

Ita ma maidakin Mataimakin Shugaban Kasar ta wallafa labarin a shafinta na Instagram, tana godiya ga Allah da “wannan kyauta mai daraja ta da namiji da yayanmu Seun da Damilola Bakare suka haifa yau Litinin”.

A watan Maris na shekarar 2018 ne dai aka daura auren Seun da Damilola a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.