✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An hako kayan aikin gonar da suka shafe shekara 2,100 binne a Isra’ila

Masanan sun yi ittifakin kayan sun shafe wadannan shekarun a kasa

Masu bincike a kasar Isra’ila sun gano wasu kayan aikin gona a Arewacin kasar da suka yi ittifakin sun shafe shekara 2,100 binne a cikin wata gona a kasar.

Daga cikin kayayyakin da aka hako har da tulunan kasa da gatura da sauran kayayyaki, kamar yadda Hukumar Binciken Isra’ila ta sanar a ranar Laraba.

Kazalika, daga cikin kayayyakin da aka gano har da wasu kwandaloli da aka tabbatar an yi amfani da su kusan shekara 100 kafin zuwan Annabi Isah (A.S)

“Mun kuma sami nasarar hako wata kwaya da ta daskare tun a wancan lokacin, kuka bincike ya tabbatar da cewa mazauna yankin ne suka tafi suka bar ta,” inji Amani Abu-Hamid, Daraktan binciken a cikin wata sanarwa.

“Bisa ga dukkan alamu sun tafi sun bar kayan ne saboda fargabar wani hatsari da ya tunkare su, watakila na harin sojoji.”

An dai hako kayayyakin ne yayin wani haka da ake yi gabanin fara wani aiki a kogin Galilee da ke Arewacin kasar.

Ana dai kokarin janyo wani ruwa ne da ba shi da gishiri-gishiri zuwa yankin lokacin da aka hako kayayyakin.

Gonar na yammacin kogin da ake kokarin janyo ruwan ne. (NAN)