✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An Hako Lu’ulu Ma Fi Girma A shekara 300 A Tarihi

Wanda bai kai shi a girma ba an sayar da shi sama da Naira biliyan daya a shekarar 2017

Masu hakar ma’adinai a kasar Angola sun hako wani  lu’ulu’u da babu kamarsa a yanzu a duniya, wanda rabon da a samu kamarsa tun shekara 300 da suka wuce.

An hako wannan nau’in dutse mai daraja ne a wata mahakar ma’adinai ta Lulo Alluvia da ke Arewa maso Gabashin kasar Angola a ranar Laraba.

Lu’ulu’un mai launin ja-ja ya kai nauyin karat 170, an kuma sa masa suna ‘Lulo pink Rose’ a cewar wani rahoto na BBC.

A wata sanarwa da ya fitar, Ministan Albrkatun Kasar Angola, Diamantino Azevedo, ya ce, “Katari da wannan dutse mai daraja na nuna irin albarkatun da kasar ke da shi a Afirka”.

A baya, an sayar da kwatankwatacin wannan dutse mai daraja da tsadar gaske.

A shekarar 2017 an sayar da wani lu’ulu’u mai nauyin karat 59 kan kudi Dala miliyan 71.2 wanda ake ganin ya fi kowanne tsada a duniya har yanzu.