✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An hana ba da izinin sa wa motoci bakin gilashi

Za a fitar da sabbin ka’idojin amfani da lambar SPY da bakin gilashin mota.

Shugaban ’Yan Sandan Najeriya, Usman Baba Alkali ya hana ba da izinin sa wa motoci bakin gilashi.

Ya kuma hana Kwamishinonin ’Yan Sandan jihohi da Mataimakan Sufeto Janar masu kula da shiyyoyi bayar da lambobin ‘Spy’.

A zaman da ya yi da su a Abuja, IGP Usman Baba Alkali ya kuma umarce su da su tabbatar da bin umarnin da kuma tsare masu rufe lambobin motocinsu ba bisa ka’ida ba.

Ya ce ana bayar da lambobin ‘Spy’ ne kawai ga wasu hukumomi bisa wasu sharudda; sannan ba kara zube ake sahale amfani da bakin gilashin mota ba.

A cewarsa umarnin nasa ya zama jazaman saboda rahotannin da ke nuna yadda ake wulakanta hurumin lambobin na ‘Spy’ da bakin gilashin da aka mayar abin nuna isa da ma aikata laifi.

Shugaban ’yan sandan ya ce nan gaba za a fitar da sabbin dokokin ba da izinin amfanin da su wadanda Rundunar za ta yi aiki kafada da kafada da Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) wajen tsarawa.

Ya bayyana wa taron fushinsa kan abin ya ce gidadanci ne, kafa shingayen binciken da ’yan sanda ke yi a kan hanyoyi.

Ya jaddada umarnin rufe dukkanninsu tare da hukunta masu kunnen kashi wurin kafa shingayen da ya ce sun zama wuraren karbar nagoro, wanda ke kara rashin yarda tsakanin mutane da ’yan jami’an ’yan sanda.