✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘An hana mu gawar ’yan uwanmu mako 1 bayan kashe su’

Gwamnati da sojoji sun tabbatar cewa Fulanin da aka ga sojoji sun loda a mata ba masu laifi ba ne

Iyalan wasu Fulanin da wasu ’yan banga suka kai wa hari bisa kuskure sun nemi gwamnati da hukumar soji su sakar musu gawarwakin ’yan uwansu da ’yan bangar suka kashe domin su yi maso sutura.

Fulanin da ke zaune wat ruka ga yankin Kakura a Karamar Hukumar Chikun a  Jihar Kaduna, sun kuma bukaci gwamnati ta ba su damar ziyartar ’yan uwansu da ke kwance a asibiti domin sanin halin da suke ciki.

A makon jiya ne dai wani bidiyo ya bayyana a kafofin sada zumunta, yana nuna sojoji na loda wasu Fulani a kan juna a cikin mota, kan zargin su da ayyukan ’yan bindiga.

Daga baya, Gwamnatin Jihar Kaduna da sojoji sun fito sun bayyana cewa Fulanin ba ’yan ta’adda ba ne kamar yadda aka rika yadawa.

Gwamnatin da sojojin sun ce Fulanin makiyayya ne da suka fito neman wasu shanunsu da aka sace da dare, amma suka yi kicibus da ’yan banga da ke neman wadansu mahara da suka kashe dan uwan basaraken yankin a lokacin.

’Yan banga sun kai hari a rugar Fulanin bayan an kashe dan uwan wani basarake a kauyen Kakura da dare, su kuma Fulanin a lokacin sun fito neman wasu shanunsu da aka sace.

Kawo yanzu an tabbatar da rasuwar mutum uku daga cikin Fulanin, wasu 14 da aka tsare kuma suna kwance a Asibitin Sojoji na 44 da ke Kaduna suna karbar magani —Amma Fulanin na zargin wadanda suka rasu sun fi haka.

Aminiya a rufar Kakura

Aminiya ta ziyarci rugar, inda ta gana da wakilin Fulanin, Yusuf Shehu, wanda ya ce tun bayan harin da aka kai musu har yanzu ba su samu damar ganin ’yan uwan nasu da ke kwance a asibiti ba.

A cewarsa, duk kokarin da suka yi don a bari su ziyarci marasa lafiyan ya ci tura duk kuwa da cewa gwamnati ta tabbatar da ba masu laifi ba ne.

Ya kuma ce mata da tsofaffi a rugar sun shiga damuwa bisa rashin sanin halin da mazajensu da ’ya’yansu ke ciki a halin yanzu.

A cewarsa, hatta gawarwakin ba su samu gani ba, ballantana su san wadanda suka rasu a cikin su.

“Muna rokon gwamnati da ta ba mu damar zuwa mu ga ’yan uwanmu da suka samu rauni, su kuma wadanda suka rasu a ba mu gawarwakin domin a yi musu sutura kamar yadda addinin Musulunci ya tanada,” inji shi.

Shugaban Karamar Hukumar Chikun, Salasi Nuhu Musa, ya tabbatar wa Aminiya cewa ya riga ya sanya hannun a takardar da DPO na ’yan sandan unguwar Sabuwar Kaduna ya aiko mishi domin a bai wa Fulanin gawarwakin wadanda suka rasu.

Ya bayyana mamakinsa cewa har zuwa lokacin ba a ba su gawarwakin ba, domin har ya tura tawagarsa sun je rugar sun jajanta wa Fulanin a kan abin da ya faru.