✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An haramta cire tsabar kudi daga asusun gwamnati

Sabuwar dokar ta haramta biyan jami’an gwamnati alawus din tafiyar aiki da tsabar kudi

Hukumar da ke sanya ido kan hada-hadar kudade a Najeriya (NFIU) ta haramta cire tsabar kudi daga asusun Gwamnatin Tarayya da jihohi da kuma kananan hukumomi daga ranar 1 ga watan Maris, 2023.

NFIU ta ce daga ranar, laifi ne a biyan ma’aikatan gwamnati alawus-alawus din tafiyar aiki a cikin gida ko zuwa kasashen waje da tsabar kudi.

Babban Daraktan hukumar, Modibbo Tukur, ne ya bayyana haka a Abuja ranar alhamis, inda ya ce karin wasu sabbin tsare-tsaren na tafe.

Ya ce za a fara amfani da sabbin tsare-tsaren ne bayan fara aikinsa dokar Babban Bankin Najeriya (CBN) na takaita cirar tsabar kudi ga daidaikun mutane da kamfanoni a Najeriya.

Da yake karin haske kan dokokin, Modibbo ya ce hakan yayi daidai da sashi na 3(1)a-s, da sashi na 23(2) na kundin hukumar.

A baya dai bisa dalilai daban-daban, ma’aikatun gwamnati da hukumomi, na fitar da kudade daga bankuna don yin mu’amalar kasuwanci a hukumance da ba a iya ganowa cikin sauki, maimakon ta hanyar musayar bankuna.