✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An haramta wa yara aikin karfi bayan mutuwar takwas a Kaduna

An dakatar da yin amfani da kananan yara daga yin aikin karfi musamman a gonaki a Karamar Hukumar Kubau ta Jihar Kaduna. Shugaban Karamar Hukumar,…

An dakatar da yin amfani da kananan yara daga yin aikin karfi musamman a gonaki a Karamar Hukumar Kubau ta Jihar Kaduna.

Shugaban Karamar Hukumar, Alhaji Sabo Aminu Anchau, ya sanar da hakan yayin zantawa da manema labarai a ranar Laraba a Kaduna.

Alhaji Sabo ya fayyace yadda wasu almajarai takwas suka mutu a hatsarin jirgin ruwa a kan hanyarsu ta dawowa daga yi wa malamansu aikatau a gonaki.

Yayin da yake bayyana bacin ransa, Alhaji Sabo ya ce galibin malaman makarantun allo na tara almajirai ne kawai da zummar su rika yi masu kwadago a gonakinsu.

Ya ci gaba da cewa ba wai suna kyamatar karatun allo ba ne, sai dai suna kokarin ganin an tsaftace tsarin almajiranci tare da inganta shi ta yadda zai amfani manyan gobe.