✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An harbe dan sanda an tsere da bindigarsa

An yi masa kwanton bauna bayan ya kai mai laifi caji ofis a Kafanchan

An bindige wani dan sanda sannan aka yi awon gaba da bindigarsa kirar AK-47 a garin Kafanchan, hedikwatar Karamar Hukumar Jema’a ta Jihar Kaduna ranar asabar da dare.

Dan Sandan mai suna Sajen John Auta yana aiki ne a wani otal mallakin Sanatan Kudancin Kaduna mai suna Wonderland Annex da ke layin Ogbomosho a garin.

Majiyar Aminiya ta ce dan sandan ya kai wani da ake zargi ne da laifin shan tabar wiwi ne zuwa ofishin yanki na Kafanchan.

A kan hanyarsa ta dawowa ne aka yi masa kwanton bauna ina aka tsinci gawarsa daga baya dauke da raunin harbin bindiga.

Yayin da Aminiya ta tuntubi kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige kan batun, ya ce bai samu cikakken rahoto ba zuwa lokacin hada wannan rahoton amma zai tuntube mu da zarar ya samu.