✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An harbe mutanen da suka kunna kida a wajen biki a Afghanistan

Maharan dai sun yi ikirarin sun 'yan Taliban ne, amma ba a kai ga tantance haka ba.

Akalla mutum uku ne rahotanni suka tabbatar an harbe a wajen wani biki saboda sun kunna kida a a Gabashin Afghanistan ranar Juma’a.

Kakakin Taliban, Zabihullah Mujahid ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai ranar Lahadi.

 A cewarsa, wasu ’yan bindiga da suka yi ikirarin ’yan Taliban ne suka kai harin, sannan suka bude wuta a wajen.

Wani dan jarida da ke aiki a yankin ya ce mutum biyu sun mutu a harin, wasu 10 kuma sun jikkata.

Kakakin ya ce an kai harin ne a gundumar Surkh Rod da ke lardin Nangarhar na kasar.

Ya ce babu wanda yake da damar kashe kowa saboda kunna kida, kuma ana ci gaba da bincike don gano ko an yi kisan ne saboda dalilai na kashin kai.

“A Jamhuriyar Musulunci ta Afghnistan, babu wanda yake da damar hana sauraron kida ta dole, sai dai kawai ya yi kokarin jawo hankalinsu su daina. Wannan shi ne abin da muke yi,” inji Zabihullah, a zantawarsa da Kamfanin Dillancin Labarai na AFP.

Kazalika, a jerin wasu sakonni da ya wallafa a shafin Twitter, Zabihullah ya ce maharan sun yi ikirarin kasancewa ’yan Taliban, inda suka bukaci a kashe kidan kafin su kai ga bude wuta, amma ba su tabbatar da ko ’yan Taliban din ba ne ko a’a.

Ya ce tuni aka cafke mutum biyu da ake zargi da hannu a cikin harin, amma mutum na ukun ya tsere.

Ko da yake Taliban ta haramta kunna kade-kade a wajen taruka, amma babu wata doka da ta fitar domin hukunta wadanda suka kunna.