✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An harbe mutum 7 har lahira a kauyen Taraba

Wannan ne karo na farko da kauyen yake fuskantar hari daga ’yan bindiga.

Akalla mutum bakwai ne wasu ’yan bindiga suka harbe har lahira a kauyen Naga da ke Karamar Hukumar Lau ta Jihar Taraba a daren ranar Talata.

Aminiya ta gano cewa ’yan bindigar, wadanda ke kan babura, sun shiga kauyen ne da wajen misalin karfe 8:00 na dare, sannan suka rika harbin kan mai uwa da wabi.

Hakan dai ya yi sanadiyyar kisan mutum bakwai, yayin da wasu da dama kuma suka jikkata.

Wani majiya daga kauyen da ya nemi a sakaya sunansa ya ce jim kadan da kammala harbe-harben, sai ’yan bindigar suka gudu cikin daji.

Ya ce wannan ne karo na farko da kauyen yake fuskantar hari daga ’yan bindiga.

Sai dai Kakakin ’yan sandan Jihar, DSP Usman Abdullahi, ya ce kauyen na Naga da aka kai harin a Jihar Adamawa yake ba Taraba ba.

“Ya kamata ku san cewa yankin (Naga) da lamarin ya faru a Jihar Adamawa yake ba a Taraba ba,” inji DSP Usman.