✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An harbe ’yan bindiga 14 da suka kai hari caji ofis a Binuwai

Lamarin dai ya faru ne a garin Katsina-Ala da ke Jihar da safiyar Lahadi.

’Yan sanda a Jihar Binuwai sun tabbatar da kashe ’yan bindiga 14 yayin musayar wuta a yunkurinsu na kai hari kan wani caji ofis a Jihar.

Lamarin dai ya faru ne a garin Katsina-Ala da ke Jihar da safiyar ranar Lahadi.

Kakakin rundunar, DSP Kate Anene, wanda ya tabbatar da lamarin, ya ce tun da farko dai ’yan sanda sun kama wadansu da ake zargin ’yan bindiga ne inda aka tsare su a caji ofis na garin Katsina-Ala domin gudanar da bincike.

Sai dai a cewarsa, da misalin karfe daya na daren Lahadi wadansu ’yan bindigar da yawansu ya kai kusan 50 sun kaddamar da mummunan hari kan caji ofis din, a yunkurinsu na kwato wadanda aka tsare a caji ofis din.

Kakakin ya ce jami’an tsaron da ke aiki a lokacin wadanda ke zaune cikin shiri sun tunkari ’yan bindigar inda suka hallaka 14 daga cikinsu a yayin musayar wutar.

Sai dai ya ce wasu daga cikinsu kuma sun tsere da raunukan harsashi.

’Yan sandan sun bukaci al’ummar garin na Katsina Ala da su ci gaba da kwantar da hankulansu sannan su ci gaba da taimaka wa rundunar da muhimman bayanai.