✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An harbi jirgin da ya je kwashe ’yan Turkiyya a Sudan

An harbi jirgin kasar Turkiyya da ya je kwashe ’yan kasar da suka makale a Sudan bayan bangarorin da ke yakar juna sun amince su…

An harbi jirgin kasar Turkiyya da ya je kwashe ’yan kasar da suka makale a Sudan bayan bangarorin da ke yakar juna sun amince su kara tsagaita wuta na tsawon awa 72.

Harbin ya sa jirgin, samfurin C-130 yin saukar gaggawa a filin jirgi na Wadi Seyidna da ke Khartoum, babban birnin kasar.

Ma’aikatar tsaro ta Turkiyya ta tabbatar da harin, sai dai ta bayyana cewa ba a samu asarar rai ko rauni ba, amma jirgin yana bukatar gyara.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito rundunar sojin kasar tana zargin rundunar ’yan sa-kai na RSF da harbin jirgin a lokacin da yake sauka a safiyar Juma’a, inda suka lalata hanyoyin man jirgin.

Sojojin sun kara da cewa ana gyaran jirgin a filin da ya sauka, saboda harbin da aka yi masa.

Amma RSF ta musanta hannunta a harbin jirgin, wanda ta kira makircin bangaren sojojin domin goga mata kashi kaji.

Wannan kuwa na zuwa ne bayan a daren Alhamis bangarorin biyu da ke yakar juna kan shugabancin kasar sun amince su tsagaita wuta na kwana uku domin ba da samar ayyukan ceto da kuma kwashe fararen hula.

Sai dai duk da haka an ci gaba da gwabza fada a tsakaninsu a Khartoum zuwa safiyar Juma’a.

Tsagaita wuta da bangarorin suka yi a baya ya ba wa dubban mutane damar ficewa daga Khartoum, birnin da ake gwabza fadan.

Kawo yanzu an kashe daruruwan mutane tun bayan barkewar yakin mako biyu da suka gabata, baya ga raba wasu dabbai da gidajensu.

Lamarin ya jefa mazauna birnin Khartoum mai yawan al’umma sama da miliyan 10 cikin halin rashin abinci da ruwan sha da sauran bukatun yau da kullum.