✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An harbi tsohon fira ministan Japan Shinzo Abe a bainar jama’a

Ana fargabar tsohon Fira Ministan Japan, Shinzo Abe, ya rasu bayan an bude mishi wuta a bainar jama'a.

Ana fargabar tsohon Fira Ministan Japan, Shinzo Abe, ya rasu bayan an bude mishi wuta a bainar jama’a.

Mista Shinzo Abe ya fadi a kasa bayan wani mahari ya bude mishi wuta ranar Juma’a a wurin yankin neman zabe a yankin Nara.

Wani ganau taron ya ce, “Yana cikin gabatar da jawabi a wurin taron ne wani mutum ya bullo daga baya,” ya bude mishi wuta, kamar yadda kafar yada labaran gwamnatin Japan, NHK ta bayyana.

NHK ta ce ’yan sanda sun tsare wani mutum mai kimanin shekara 40 bisa zargin kisa, kuma an kwace wata bindiga a hannunsa.

Rahotanni sun ce Mista Abe, wanda shi ne wanda ya fi dadewa a kan kujerar Fira Ministan Japan, yana cikin mawuyacin hali, kuma bugawar zuciyarsa ta yi rauni.