✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An janye dakatarwar da aka yi wa Shugaban Majalisar Dokokin Filato

An dage hukuncin bayan wata biyar da dakatar da su daga halartar zaman majalisar.

Majalisar Dokokin Jihar Filato ta janye dakatarwa da ta yi wa shugabanta, Abok Nuhu Ayuba da wasu mambobinta biyar.

An dakatar da Abok da sauran ’yan majalisar ne bayan wani taro da suka gudanar a dakin taro na Zawan da ke Jos ta Kudu, lokacin da rikicin kabilanci ya addabi jihar a shekarar da ta gabata.

Majalisar, karkashin jagorancin Yakubu Sanda, ta ce ta yi duba kan hukuncin da aka dauka kan shugaban nata, wanda ta ce ya saba da doka sannan ta bayar da umarnin janye dakatarwar.

Dage hukuncin na zuwa ne bayan kuduri da Mataimakin Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dokokin Jihar Filato, Philip Wallok, ya mika a ranar Alhamis.

Wallok ya bayyana cewa bayan daukar lokaci ana takfa muhawara tare da amincewa, ya bukaci majalisar ta ba su dama su ci gaba da halartar zaman majalisar.

Bayan sauraren ra’ayoyin mambobinta, majalisar ta amince tare da janye hukuncin da aka zartar wata biyar da suka shude.

Wakilinmu ya rawaito cewa wadanda hukuncin ya shafa a baya sun hada da Nuhu Abok Ayuba, marigayi Henry Longs, Dangtong Timothy, Musa Agah, Bala Fwanje da kuma Nanbol Listic.