✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An janye dokar sanya takunkumi a Ghana

Babu bukatar gabatar da katin shaidar allurar rigakafin Coronavirus ga matafiyan da suka isa kasar.

Gwamnatin Ghana ta sanar da janye dokar sanya takunkumi a duk fadin kasar.

Shugaba Nana Akufo-Addo ne ya sanar da matakin a ranar Lahadi, yana mai cewa a yanzu an samu raguwa sosai na masu kamuwa da cutar Coronavirus.

Kazalika shugaban ya kuma cire bukatar gabatar da katin shaidar allurar rigakafin Coronavirus ga matafiyan da suka isa kasar a filin jirgin saman kasar da ke Accra.

Daga nan ya bukaci al’ummar kasar da su ci gaba da kula da tsabtar kansu da ma muhallansu da kuma kaucewa shiga taron jama’a.

BBC ya ruwaito cewa adadin masu kamuwa da cutar ya fara raguwa sosai tun daga karshen shekarar da ta wuce.

Ya zuwa yanzu an samu mutum kusan dubu dari da sittin da daya da suka taba kamuwa da Coronavirus a kasar.

Ghana dai ta shiga cikin jerin kasashen Afirka da suka sassauta dokokin korona duk da gargadin da Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi cewa dage dokokin ya yi kusa.

A bayan nan ne dai Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce cutar Coronavirus ta sake karuwa a cikin wasu kasashen Turai wadanda suka yi gaggawar soke matakan rigakafi na yaki da annobar.

Darektan WHO Reshen Turai Hans Kluge ya ce Coronavirus ta sake yaduwa a karkashin nau’in BA2 a Jamus da Birtaniya da Faransa da Italiya da cikin wasu kasashen guda 18 cikin 53 da ke yankin na Turai.