✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An janye karar da ta hana a yi mukabalar Sheikh Abduljabbar

Sai dai Gwamnatin Kano ba ta ce uffan game da hukuncin kotun ba.

Wani lauya a Jihar Kano da ya nemi a haramta mukabala tsakanin Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara da sauran malamai a yanzu ya janye kararsa da daga gaban alkali.

A yanzu alamu na nuna cewa mukabalar za ta gudana sai dai har kawo yanzu gwamnatin Kano ba ta ce uffan game da hukuncin kotun ba.

Barista Ma’aruf Yakasai shi ne lauyan da ya gabatar da karar a gaban kotun da ke Gidan Murtala kana daga bisani ya janye.

Lauyan a watan Fabrairun da ya gabata ne ya nemi kotun da ta haramta mukabalar tsakanin Sheikh Abduljabbar da sauran malaman Kano yayin da ya rage kwanaki biyu kacal ta gudana.

Sai dai lauyan a ranar Litinin ta bakin mai wakiltarsa a gaban kotu, Barista Lukman Auwal Abdullah, ya sanar da janye karar da shigar bisa la’akari yadda al’ummar Kano suka nuna sha’awarsu don ganin mukabalar ta tabbata.

A watan Janairun da ya gabata ne Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya haramta wa Sheikh Abduljabbar yin wa’azi da sauran karatuttukansa gami da rufe masallacinsa har sai abin da hali ya yi.

A kwanan baya Gwamnatin Jihar Kano ta sanya ranar Lahadi, 7 ga watan Maris na 2021 a matsayin ranar da za a gudanar da mukabala tsakanin Sheikh Abduljabbar da Malamai a Jihar.