✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kaddamar da kasuwar kayan abinci ta tafi-da-gidanka a Legas

Shugabanin kasuwar kayan gwari da sauran nau’in kayayyakin abinci ta duniya da ke unguwar mile 12 a Legas sun kaddamar da kasuwar tafi-da-gidanka domin bai…

Shugabanin kasuwar kayan gwari da sauran nau’in kayayyakin abinci ta duniya da ke unguwar mile 12 a Legas sun kaddamar da kasuwar tafi-da-gidanka domin bai wa al’umar jihar Legas damar sayan kayayyakin abinci daga gidajen su a lokacin dokar hana fita domin dakile annobar Coronavirus.

Shugaban kasuwar Alhaji Usman Shehu Samfan, ya shaida wa Aminiya cewa sun kaddamar da kasuwar kayan abinci ne ta tafi-da-gidanka biyo bayan dokar da gwamnatin tarayya ta kafa na hana fita a jihohin Legas da Abuja.

Ya ce, akwai lambobin waya da suka tanada na musamman da kuma adireshin yanar gizo wanda za a shiga ko a kira lambar waya ayi odar kayan abinci da suka hadar da: kayan miya da hatsi da sauran nau’in kayayyakin abinci ga masu sayan kadan ko da yawa.

 

Wasu daga cikin kayan abincin.