An kaddamar da rigakafin COVID-19 zagaye na 3 a Najeriya | Aminiya

An kaddamar da rigakafin COVID-19 zagaye na 3 a Najeriya

Rigakafin COVID-19 na kamfanin Pfizer
Rigakafin COVID-19 na kamfanin Pfizer
    Abubakar Muhammad Usman

A ranar Juma’a Gwamnatin Tarayya ta kaddamar shirin bayar da allurar rigakafin COVID-19 zagaye na uku, bayan da nau’in kwayar cutar na Omicron ya bulla.

A ranar Alhamis ne Daraktan Lafiya a Matakin Farko, Dakta Faisal Shuaib ya sanar da shirin fara zagaye na ukun, a sansanin ’yan gudun hijira a Abuja.

Shuaib ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta yanke shawarar amfani da rigakafin kamfanin Pfizer Bio-N-tech a zagaye na ukun.

Tuni wasu kasashen duniya suka fara rigakafin zagaye na uku domin kara karfin rigakafin a jikin wadanda aka yi wa zagayen farko da na biyu.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), ta shawarci mutane su karbi allurar rigakafin, musamman a nahiyar Afrika, wadda a nan ne aka fi samun masu dauke da sabon nau’in cutar na Omicron.