✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kafa dokar hana fita ta sa’o’i 24 a Kuros Riba

Masu zanga-zangar sun kone wani gidan mai mallakar Gwamna Ben Ayade.

Gwamnan Jihar Kuros Riba, Farfesa Ben Ayade ya kafa dokar hana fita ta tsawon Awa ashirin da hudu bayan da masu zanga-zanga suka shafe yinin Juma’a har zuwa safiyar Asabar suna cin karensu babu babbaka.

Hakan na zuwa ne bayan da rahotanni suka bayyana cewa akalla mutum biyar sun mutu a ranar Juma’a yayin da masu zanga-zangar #EndSARS da zauna gari banza suka yi wawoson dukiya da kayan abincin da Gwamnatin Tarayya ta bayar tallafi domin rage radadin annobar coronavirus.

Mutum uku sun mutu yayin da aka cinna wuta a ofishin Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Kuros Riba (SEMA) inda aka ceto wasu mutane bayan sun shaki hayaki.

A safiyar Asabar, masu zanga-zangar sun kone wani gidan mai mallakar Gwamna Ben Ayade.

Ba su tsaya nan ba, sun koma gidajen Sanatoci masu ci yanzu da suka hadar da gidan Sanata Genshom Bassey da ke Asari Edo da na Sanata Victor Ndoma Egba.

Kazalika bayan kona bankin First Bank reshen 8miles a Kalaba a ranar Asabar, sun kuma kai hari didan dan Majalisar Wakilai, Essien Ayi.

Haka Kuma sun koma kantin zamani na matar tsohon Gwamnan Jihar Kuros Riba Sanata Liyel Imoke sannan suka fantsama sauran wurare a birnin Kalaba suna ci gaba da tafka ta’asa.

Daga cikin sauran wuraren da aka kai hari sun hadar da Ofishin Hukumar Kwadago (NLC), da na Hukumar Zabe (INEC) da kuma Ofishin ‘Yan Sanda na Atakpa.