✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kafa hukumar kula da amfani da tabar wiwi wajen sarrafa magani a Morocco

A shekarar 1954 ne aka haramta noman wiwi a Morocco.

Hukumar da ke sa ido kan yadda ake amfani da tabar wiwi wajen sarrafa magani ta kasar Morocco ta gana a karon farko game da daya daga cikin matakan karshe kafin ba da izinin amfani da tabar a kasar.

Kasar da ke Arewacin Afirka ta amince da wata doka a shekarar 2021 na dan wani lokaci da ke ba da izinin yin amfani da tabar wiwi wajen sarrafa magani, kayan kwalliya da amfanin masana’antu, inda ta kafa wata hukuma ta musamman da za ta rika sanya idanu a kai.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Abdelouafi Laftit ya jagoranci hukumar, domin amincewa da jadawalin takwarorinta na duniya, tare da ware kasafinta na shekarar 2022.

Hukumar za ta dauki nauyin kula da duk matakan da ake nomawa, tun daga shigo da iri zuwa sayar da kayayyakin wiwi kamar yadda Gidan Rediyo Faransa na RFI ya ruwaito.

Hakanan za ta rika sanya ido kan hanyoyin ba da izini ga ma’aikata na kasar da na duniya a cikin masana’antun da ke sarrafa wiwi a hukumance.

An kiyasta tabar wiwin da ake nomawa a Arewacin Afirka sama da tan 700 cikin wani bincike na 2020 da kungiyar yaki da aikata manyan laifuka ta duniya ta fitar.

Dangane da rahoton 2020 na Majalisar Dinkin Duniya kan yadda ake sarrafa magunguna da aikata Laifuka kuwa, Morocco ita ce mafi girma a duniya da ke samar da nau’ikan tabar wiwi daban-daban.

A shekarar 1954 ne aka haramta noman wiwi a Morocco, amma an samar da wasu sauye-sauye saboda noman wiwin na taimakawa iyalai akalla 60,000, inda suke noma a kusan kadada 55,000.