✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kafa kotunan hukunta masu saba dokar COVID-19

Jihar Imo ta kafa kotunan tafi-da-gidanka don hukunta masu kunnen kashi

Gwamnatin Imo ta kafa kotunan tafi-da-gidanka don hukunta masu karya dokokin kariyar cutar COVID-19 da aka shimfida a Jihar.

Ta kuma umarci jama’ar Jihar da su kiyaye matakan kariyar cutar COVID-19 saboda hadarinta da cutar ke dauke da shi.

Tana kuma umartar masu wuraren kasuwanci da wuraren taruwar jama’a da daidaikun mutane su tabbatar da bin matakan kariyar cutar.

Sanarwar da Mashawarcin Gwamnan kan Kariya ta musamman, Ugochukwu Nzekwe, ya fitar ta kuma bukaci mutane su ringa sanya safar rufe baki da hanci da wanke hannuwansu da goga man sinadarin tsaftace hannu da kuma bayar da tazara a wuraren taruwar jama’a.  

Sannan kuma jama’a su kaurace wa wuraren da aka tara sama da mutane 100.

Har-ila-yau sanarwar ta bawa ma’aikatan umarnin zama a gida daga ranar Talata 22, ga Disamba, 2020, don su gudanar da bukunkuwansu na Kirsimeti da Sabuwar Shekara.