✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kafa kungiyar ’yan jaridar intanet a Kano

An kafa kungiyar 'yan jaridu da za ta rika lura da kafafen watsa labarai na yanar-gizo.

’Yan jarida a jihar Kano sun kirkiro wata kungiya da za ta daidaita al’amuran kafafen yada labarai na intanet.

An gudanar da zaben Shugabannin kungiyar ne a ranar Asabar, kuma shi ne karo na farko da aka samar da wata kungiya domin kula da kafafen watsa labarai na intanet a jihar.

Wadanda aka zaba a matsayin shugabannin kungiyar sun hada da, Hisham Habib daga News Tunnel, Shugaba; Nazifi Dawud daga DailyFocus, Mataimakin Shugaba; da Yakubu Salisu daga Metro Daily, Sakatare.

Sauran sun hada da Abbas Yusha’u na Nigerian Tracker,  Mataimakin Sakatare; Mukhtar Yahaya Usman na Kano Focus, Sakataren Kudi; Zainab Mai Agogo daga White Blood Multimedia, Ma’aji; da Muhammad Buhari Abba daga Labarai24, Mai Binciken Kudi.

Zababbun shugabannin sabuwar kungiyar ana sa ran za a kaddamar da su a ranar Litinin, 16 ga Nuwamba.