✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kai hari a rugar Fulani a Abuja

’Yan bindiga sun kai hari a wata rugar Fulani inda suka bindige wani matashin makiyayi a Abuja.

’Yan bindiga sun kai hari a wata rugar Fulani inda suka bindige wani matashin makiyayi a Abuja.

Shaidu sun ce da zuwan ’yan bindigar rugar, sai suka harbi Abdulmumin Jagaba mai shekara 30, a goshi, nan take suka juya suka tafi.

“Da shigowarsu, sai suka harbe matashin, suka juya suka tafi, ba su dauki komai ko suka yi garkuwa da wani ba,” inji wani ganau.

Ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 11 na dare, ranar Litinin a rugar da ke kusa ne da kauyen Sabon Gari da ke Karamar Hukumar Kwali.

A cewarsa, an sanar da ’yan bindiga da ke kauyen Gada-Biyu, amma kafin su iso maharan riga sun tafi.

Ya ce DPO na Babban Ofishin ’Yanda da ke Kwali, SP Tony Obiano, da wasu jami’ansa da Ardon Kwali da ’yan banga sun ziyarci wurin inda DPO din ya dauki bayanai kafin a yi wa mamacin jana’iza.

Mun kira domin samun karin bayani daga mai magana da yawun Rundunar ’Yan Sandan Abuja, ASP Maryam Yusuf, amma wayarta na a kashe.